060511 Afghanistan 9/11 Spurensuche
August 8, 2011A tsakanin unguwannin birnin inda akasarin ƙungiyoyin agaji ke da ofisoshinsu akwai wata unguwa ɗaya dake da babakeren masu riƙe da madafun iko, amma kuma a ɗaya ɓangaren talakawa na da damar gabatar da koke-kokensu a wannan unguwa mai suna Karte Seh dake yammacin Kabul.
Ayyukan gine-gine na tafiya gadan-gadan a unguwar Karte Seh. Unguwar baki ɗayanta ta zama wani dandalin gine-gine. Hakan kuwa wani babban ci gaba ne ga birnin na Kabul saboda kasancewar a duk inda aka ce ana gini to kuwa ana zuba jari ba ƙaƙƙautawa.
Gine-ginen zamani a daura da na laka
A zamanin baya dai masu matsakaicin ƙarfi ne ke da ikon zama a unguwar ta Karte Seh, inda zaka tarar da ɗaiɗaikun gidaje da aka ƙawata su gwanin kyau. Daga baya aka fara samun gidajen bukkoki na laka sakamakon yaƙin ƙasar Afganistan da ya tilasta mazauna karkara kutsawa zuwa birnin Kabul. Amma a halin da ake ciki yanzun an shiga wani sabon yayi, inda ake gina ƙasaitattun gidaje irin shigen na Pakistan. Ɓangarorin unguwar guda biyu, ɓangaren masu hannu da shuni da na talakawa 'yan rabbana ka wadata mu sun haɗu ne a wata gada mai suna Pol-e-sork, wato jar gada. Za dai ka tarar da mutane da ƙabilu daban-daban a wannan unguwar, ko da yake da ƙyar mutum kan ga mata a cikin burƙa.
A wata kasuwa ta unguwar ana sayar da kayan marmari ri-iri, kuma kowane daga masu tebur a kasuwar na da labarinsa dangane da Taliban:
"Ni ne Haji Murad Ali. Sau 32 'yan Taliban na cin zarafi na."
Taliban na ganin ƙyashin duk wani mai abin hannunsa
Haji Murad Ali yana da kantin sayar da kayan halawa, ya kuma ƙara da bayani yana mai cewar:
"Taliban kan tinkari mutum da zarar sun ganka da sabuwar riga, inda suke iƙirarin cewar wai kai mawadacin kwamanda ne. Nan take za su fara dukan mutum da kulki. Su kan azabtar da mutane su riƙa dariyar ƙeta. Su kan watsa wa mutum ruwa mai raɗaɗin sanyi. Duka-duka maganar kuɗi kawai ta dame su. Ka gane?"
Bisa ta bakin Haji Murad Ali, an yi masa sata a 'yan makonnin da suka wuce, a yayinda ya kira 'yan sanda sai suka nemi toshiyar baki daga gare shi a maimakon su taimaka masa. A na su ɓangaren ma dai sace masa wasu 'yan kaya suka yi daga shagonsa. Ya ce in kuma ka kuskura ka yi magana sai su tasa ƙeyarka zuwa kurkuku. Shi kuwa Sanjar ɗan Afganistan dake auren wata 'yar Rasha mai suna Sonia, mamaki yayi da maƙobcinsu yana mai cewar.
'Yan majalisa na azurta kansu da kansu
"Maƙobcinmu ɗan majalisa ne, kuma a cikin ƙiftawa da bisimilla ya kuɗance, alhali ya fito ne daga karkara. Ganin haka tilas mutum ya riƙa saka ayar tambaya game da cewar daga ina waɗannan kuɗi suka fito, a matsayinsa na ma'aikacin gwamnati."
Bisa ga ra'ayin Sanjar ita kanta majalisar ce ummal'aba'isin yaƙin basasar Afghanistan a farkon shekarun 1990.
"'Yan kisan kai ne kawai suka cika wannan majalisar. Su ne ainihin mutanen da suka ɓannatar da wannan unguwar a wancan lokaci. Su ne ke da alhakin mutane dubu 60 da suka rasa rayukansu. Su ne suka buɗe mana wuta lokacin da muke fafutukar kai wa mutane taimakon hatsi. A yau su ne wakilan majalisa kuma 'yan diplomasiyyar yammaci na yaba musu da kasancewa wata sabuwar alama ta demokraɗiyya. Wace irin demokraɗiyya? Kamata yayi a gurfanar da waɗannan mutanen gaban kuliya."
Mawallafa: Martin Gerner / Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal