SiyasaAmurka
FBI ta kori jami'anta da suka fallasa shugaba Trump
February 26, 2026
Talla
Hukumar binciken tsaro ta Amurka FBI ta kori jami'anta shida daga aiki, bayan samunsu da laifin fallasa yadda shugaba Donald Trump ya boye wasu kundayen bayanan tsaro a gidansa na Mar-a-Lago a Florida, bayan kwashe su daga fadar White House, lokacin da ya sha kayi a zaben shugaban kasa na 2020.
Shugaban hukumar Kash Patel ne ya ba da umarnin korar ma'aikatan, bisa rawar da suka taka a badakalar binciken Mr Trump ta shekarar 2022, bayan gaza samun damar zarcewa a kan kujerar shugabancin Amurka zango na biyu a jere.
Karin bayani - Trump ya bayyana nasarorin gwamnatinsa
Muhimman bayanan da Mr Trump ya boye a gidan na sa sun kunshi takardun shelkwatar tsaro ta Pentagon da kuma na hukumar leken asiri ta CIA.