1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shirya mika jagoran yakin Ruwanda a gaban kotun duniya

Ramatu Garba Baba
June 3, 2020

Kotu a kasar Faransa ta amince da ta mika Felicien Kabuga da ake zargi da laifukan yaki a Ruwanda a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya.

Gesucht-Poster Felicien Kabuga
Hoto: picture-alliance/abaca/E. Hockstein

Wata kotu a kasar Faransa ta amince da ta mika Felicien Kabuga ga kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya, sai dai ta baiyana damuwa kan halin rashin lafiyan mutumin da ya dade yana tserewa hukunci.

Ana zargin dan asalin kasar Ruwandan da laifin hannu a kisan kare dangi da kuma daukar nauyin kungiyoyi na masu dauke da makamai na 'yan kabilar Hutu a yayin rikicin kasar da ya yi sanadiyar rayukan mutum kusan miliyan daya. Tun a watan Maris da ya gabata aka cafke Kabuga a wani gari da ke yankin babban birnin Paris na kasar Faransa bayan da aka jima ana nema shi ruwa a jallo.