Felix Tshisekedi ya dora wa Joseph Kabila karar tsana
April 24, 2025
Tsamin dangantakar ta samo asali ne tun lokacin da tsohon shugaban kasar Kwango Joseph Kabila ya zargi shugaban da ya gaje shi Felix Tshisekedi da gazawa wajen gudanar da mulki, wanda hakan ya haifar da yakin da ake gwabzawa tsakanin gwamnatin Kwango da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda a gabashin kasar.
A nata bangaren, gwamnatin Kinshasa na zargin tsohon shugaban kasar da yunkurin mai da hannun agogo baya a kokarin warware takaddama a rikicin da ke tsakanin kwango da Ruwanda. Wasu sabbin matakan da gwamnatin Tshisekedi ta dauka na rage tasirin Mr. Kabila shi ne haramta ayyukan jam'iyyarsa ta PPRD a fadin kasar. Kazalika, jami'an tsaro sun kaddamar da bincike a gidan tsohon shugaban kasar da ke birnin Kinshasa.
Karin bayani: Dalilin tasirin 'yan tawayen M23 a kan sojojin Kwango
Farfesa Yvon Muya da ke bincike kan tsaro da zaman lafiya da ke Jami'ar Saint Paul a Kanada, ya ce dawowar Kabila alkhairi ne ga kasar domin zai taimaka wajen kawo karshen rikicin da ke tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye. Ya ce: "Kabila zai iya zama mafita, amma dole ne ya yi aiki da gwamnati mai ci a Kinshasa. Muryarsa na da tasiri a tsakanin al'umma. A don haka, yana da rawar da zai taka wajen tattauna wa da ‘yan tawaye da kuma ‘yan siyasan Kinshasa."
Gwamantin Tshisekedi na zargin Mr. Kabila da daukar nauyin ‘yan tawaye, musamman tsohon shugaban hukumar zaben kasar a zamanin mulkinsa Corneille Nangaa. Sai dai, masana siyasa irin su Farfesa Nkere Ntanda na Jamhuriyar Kwango ya yi kira da gwamnati da ta daina amfani da labaran shafcin gizo domin hakan ba zai haifar da ‘da mai ido ba.
Karin bayani: Mai ya hana kawo karshen rikicin Kwango?
Farfesa Nkere Ntanda ya ce: " Babu wanda yake da tabbacin yana kan hanyarsa ta zuwa Goma daga Kigali, kuma wai har ya sauka a Goma. Kawai zance ne marasa tushe. Kabila mutum ne da baya boye kansa. Ko da mulki ko kuma babu mulki."
Shugaban Kwango ya bukaci babban mai gabatar da kara na gwamnati da ya fara aiki tare da hadin gwiwa da ma'aikatar shari'a wajen gurfanar da Joseph Kabila a gaban kotu kan laifin taimaka wa ‘yan tawaye. Saboda haka ne wani dalibi mai sunha Caleb, da ke birnin Goma ya nuna takaicinsa kan yadda Kabila ke haifar da tazgaro a zaman lafiyar kasar, inda ya ce: "Abin takaici ne a ce tsohon shugaban kasa, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 18 na jagorantar ‘yan tawaye, duk da furucinsa na bukatar hadin kan kasa tsakanin al'umma, kawai saboda ya karbe madafun iko''
Karin bayani:Ilimi ya tabarbare sakamakon rikici a gabashin Kwango
Bisa jagorancin kasar Qatar, gwamnatin Kwango da ‘yan tawayen M23 sun fitar da sanarwar hadin gwiwa na amincewa da tsagaita bude wuta tare kuma da kawo karshen yakin baki daya. Ko a watan Maris, Shugaba Tshisekedi da takwaransa na Ruwanda Paul Kagame, sun yi ganawar ba za ta a birnin Doha domin kawo karshen takun-sakar da ke tsakaninsu.