SiyasaTurkiyya
Turkiyya: Rasuwar Fethullah Gülen
October 21, 2024Talla
Shi dai Marigayi Fethullah Gülen ya kasance jigo a siyasar kasar ta Turkiyya, kafin ya samu sabani da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdoğan. Gülen dai, na daga cikin wadanda gwamnatin ta zarga da yunkurin juyin mulki a shekara ta 2016. Kana marigayin ya kasance mai daya daga cikin cibiyoyin Turkawa da suke da tasiri a duniya, ciki har da rukunin makarantun Turkish International da ke kasashen Afirka kamar Najeriya.