Kasashen AES sun fice daga kotun ICC
September 23, 2025
A Jamhuriyar Nijar, 'yan kasar sun soma bayyana matsayarsu a game da matakin da kasashen Kungiyar AES na Jamhuriyar Nijar, da Mali da burkina Faso suka dauka na ficewa daga cikin kasashen membobin kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya wato ICC a bisa zarginta da kasancewa wani makami da kasashen Turawa ke amfani da su wajen ci gaba da yi wa kasashe masu karamin karfi musamman na Afirka mulkin mallaka.
A yayin da wasu ‘yan nijar ke ganin dacewar matakin da sabuwar tafiyar samar wa kasashen Afirka cikakken ‘yancin kai, wasu na bayyana matakin da wani yinkurin na shugabannin mulkin sojan kasashen na kauce wa shiga komar kotun ta ICC.
Sanarwar ficewa
A wata sanarwar hadin gwiwar shugabannin kasashen kungiyar ta AES ce wacce shugaban mulkin sojan kasar Mali kana shugaban hadakar kasashen na AES Janar Assimi Goita ya sanya wa hannu a ranar 22 ga wannan wata na Satumban 2025, kasashen na AES suka bayyana wannan mataki nasu na ficewa daga yarjejeniyar Roma ko statut de Rome wacce ta kafa kotun hukuntan manyan lafuka ta Duniya ta ICC ko CPI a Faransance.
Kasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar wadanda suka shiga yarjejeniar kafa kotun a daya bayan daya a ranar 16 ga watan Aprilun 2004, da 16 ga watan Agustan 2000 da kuma 11 ga watan Aprilun 2002, sun ce sun fice daga kotun ne a bisa zarginta da kasancewa wani makami wanda manyankasashen yammacin duniya musamman na Turai ke amfani da kotun wajen kuntata wa kasashen marasa karfi da shugabanninsu musmaman na nahiyar Afirka.
Yayin da ashare day asuka kauda gag a wasu manyan ayyukan asshan da wasu kasashen na duniya suka aikatawa kamar dai yadda Malam Bana Ibrahimwani dan fafutika da ke goyon bayan matakin ficewar kasashen na AES.
Masu adawa da ficewar
Wasu manyan kungiyoyin kare hakin dan Adam na duniya sun fitar da rahotanni masu yawa a baya inda suke zargin shugabannin mulkin sojan kasashen na AES da aikata manyan laifuka na cin zarafin dan Adam a kasashensu. Kuma Dokta Mayra Djibrin wata ‘yar fafutika ‘yan nijar da ke da zama a Faransa na ganin matakin ficewar kasashen na AES daga ICC wani yinkuri ne na kauce wa hukuncin kotun ta ICC kan shugabannin nan gaba.
Sai dai Kasashen kungiyar ta AES sun ce ba wai ficewarsu daga ICC na nufin kawo karshen kula da batun kare hakkin dan Adam ba ne a yankin nasu. Sannan a share daya suna kan shirin girka wata kotun hukuntan manyan laifukan da kare hakin dan Adam a kasashen na Sahel.