1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA ta dakatar da 'yan wasan kasar Argentina wasanni 21

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 21, 2026

Paredes ne ya fi fuskantar dakatarwar wasanni 10, tare da tarar Dalar Amurka $90,000, saboda rashin da'a a kofin duniya.

Yadda 'dan wasan Argentina Leandro Paredes ya kayar da 'dan wasan Spain Gavi a wasan karshe na kofin duniya FIFA 19.07.2026.
Yadda 'dan wasan Argentina Leandro Paredes ya kayar da 'dan wasan Spain Gavi a wasan karshe na kofin duniya FIFA 19.07.2026.Hoto: Marvin Ibo Güngör/GES/picture alliance

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta dakatar da 'yan wasan kasar Argentina da masu horaswa, har tsawon wasanni 21, bayan samunsu da laifin nuna halin rashin da'a, a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na bana, wanda Spain ta lashe kofin, a ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata, bayan doke Argentina din da ci 1-0.

Karin bayani:Xavi Hernandez ya karbi aikin horas da yan wasan Netherlands

Leandro Paredes ne 'dan wasan da ya fi shan gudumar FIFA, bayan dakatar da shi har tsawon wasanni 10, tare da cinsa tarar Dalar Amurka $90,000, sanadiyyar laifin shake wuyan 'dan wasan Spain Eric Garcia, sannan kuma ya kayar da 'dan wasa Gavi har kasa.

Karin bayani:Ba mu da kwarin giwa kan Infantio- UEFA 

Sai Nahuel Molina da aka dakatar da shi wasanni bakwai, shi ma da tarar Dalar Amurka $90,000, Thiago Almada kuwa wasa daya aka dakatar da shi da kuma tarar dala $30,000.

Karin bayani:FIFA: Guguwar sauyi na neman tafiya da Infantino 

Sai tsohon kyaftin din Argentina, kuma mataimakin mai horas da 'yan wasan kasar, wato Roberto Ayala, da ya samu dakatarwar wasanni uku da kuma tarar $30,000.

Karin bayani:UEFA za ta kauracewa gasar kofin duniya da FIFA ke shiryawa 

Haka zalika FIFA ta ci tarar hukumar kwallon kafar Argentina dala $321,000, a dalilin gaza kawwame 'yan wasanta, a lokacin da suke nuna rashin da'a a filin wasa.

Karin bayani:FIFA za ta sayar da hannun jarin kwallon kafa 

A gefe guda shi ma 'dan wasan Spain Gavi, ya samu hukuncin dakatarwar wasa daya, da kuma tarar dala $30,000, saboda rawar da ya taka a yayin tarzomar.