1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Finland ta daga kambunta na kasa mafi farin ciki a duniya

March 20, 2024

Yayin da ake gudanar da ranar farin ciki ta duniya, Finland na ci gaba da rike kambun kasar da ta fi kowacce kwanciyar hankali tare da wasu kasashen Scandinavian, acewar wani rahoton hukumar tattara alkaluman farin ciki

Matasan Finland a yayin da suke farin cikin a wani wasan kwallon hockey da suka doke Canada a 2022.
Matasan Finland a yayin da suke farin cikin a wani wasan kwallon hockey da suka doke Canada a 2022.Hoto: Jussi Nukari/Lehtikuva/AFP via Getty Images

Karo na bakwai kenan da Finland ke lashe lambar kasa mafi kwanciyar hankali da farin ciki a duniya, yayin da makwabtanta irinsu Denmark da Sweden da Iceland  suka kasance a cikin rukunin kasashe 10.  Kasashen Costa Rica da Kuwait sun shiga rukunin kasashe 20 mafiya farin ciki a duniya inda suka maye guraben Jamus da Amurka.

Karin bayani: Finland: Takaddama ta rusa gwamnati 

Kasashen Serbia da Bulgaria da Latvia dake gabashin Turai sun dan samu tagomashi na kasance a cikin kasashe mafiya farin ciki, yayinda Afganistan ta kasance kasa ta karshe.

Karin bayani: Norway ce mafi farin cikin al'umma a duniya

 Rahoton na kasashe mafi kwanciyar hankali a duniya ya zo daidai da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin gudanar da gangamin bikin ranar.