1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Finland za ta shiga NATO

Suleiman Babayo ZMA
May 12, 2022

Finland ta tabbatar da niyyar shiga kungiyar tsaro ta NATO/OTAN ba tare da bata lokaci ba, inda ake sa ran kasar Sweden ta biyo baya.

Finland | Firamnista Sanna Marin da shugaban kasa Sauli Niinistö
Firamnistan Finland Sanna Marin da shugaban kasar Sauli Niinistö Hoto: Markku Ulander/Lehtikuva/dpa/picture alliance

A wannan Alhamis kasar Finland ta tabbatar da niyyar shiga kungiyar tsaro ta NATO/OTAN ba tare da bata lokaci ba, inda ake sa ran kasar Sweden za ta bi sahu. Kasashen biyu sun kasance 'yan ba ruwanmu kan shiga wani bangare na kawance soja tun bayan yakin duniya na biyu, sakamakon makwantaka da tsohuwar Tarayyar Soviet.

Amma komai ya sauya sakamakon kutsen da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya kaddamar a kan kasar Ukraine. Tuni mahukuntan Rasha suka ce matakin shiga kungiyar tsaron NATO ga kasashen biyu na Finland da Sweden na zama barazana ga kasar ta Rasha kuma za ta mayar da martani, sai dai bata tantance irin matakin da za ta dauka ba.