Narendra Modi ya lashe zaben Indiya
May 23, 2019Talla
A wani sabon babin shugabancin wa'adi biyar nan gaba, firaiministan Indiya Narendra Modi ya samu nasara a zaben kasar mafi girma da tasiri a tarihin siyasar duniya. Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta INC Rahul Ghandhi ya amince da shan kaye a zaben, Shuga Donald Trump na Amirka da firaiministan kasar Pakistan na cikin shugabannin duniya da suka taya Narendra Modi murnan lashe zabe.
Akalla mutane miliyan 600 ne aka kiyasta suka kada kuri'a a zaben na Indiya, sai dai ana ganin samar da ayyukan yi tsakanin al'ummar kasar da sasanta rikici tsakanin Pakistan da Indiya na cikin manyan jan aikin da ke gaba firaiminsita Modi a sabon wa'adin shekaru biyar da zai yi.