1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: An kawar da batun shirya zabe nan kusa

April 12, 2024

Firaiministan Mali ya sanar da cewa gwamnatin mulkin sojin kasar ba za shirya zabe nan kusa ba don mika mulki ga farar hula har sai ta kammala saisaita lamura kamar yadda ta tsara.

Mali | Choguel Kokalla Maïga
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst des Amtes des Premierministers

A lokacin da ya ke sanar da hakan a gidan talabijin din kasar, Choguel Kokalla Maïga ya jaddata cewa dolle ne sai Mali ta dawo cikin hayyacinta kafin a yi maganar shirya zabe, sai dai ba yi karin haske kan wani kayyadaden lokaci ba.

Karin bayani: Sojojin Mali sun haramta al'amuran siyasa a fadin kasar

Mista Chogel Maiga ya kuma siffanta 'yan siyasa da a baya-bayan nan ke da'awar a gaggauta mika mulki ga farar hula a matsayin karnukan farautan wasu kasashe da ya bayyana a matsayin makiyan Mali.

Karin bayani: Rusa kungiyar dalibai ta jawo damuwa a kasar Mali

Firaiminstan ya kuma zayyana irin nasarorin da Mali ta samu na fatattakar 'yan ta'adda bayan da ta raba gari da Faransa da kuma kasashen Turai, sannan kuma ya ce sai bayan kammala zaman tattaunawa na kasa da aka fara a ranar 31 ga watan Disamba bara karshin kanal Assimi Goita ne za a san alkiblar da kasar ta dosa.