1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman Firaminista bisa zargin kisa

Ramatu Garba Baba
February 21, 2020

Mahukunta sun bayar da umarnin a kama Firaminista Thomas Thabane bayan da ya ki gurfana a wannan Juma'a a gaban kotu a bisa zargin da ake masa mai nasaba da kisan matarsa.

Lesotho Prozess Premierminister Thomas Thabane
Hoto: Reuters/Sumaya Hisham

Babban kwamishan 'yan sandan kasar Lesotho, ya bayar da umarnin a kama Firaministan Thomas Thabane bayan da ya ki gurfana yau a gaban kotu bisa zargin da ake masa, mai nasaba da kisan matarsa. Akwai rahotanni da ke nuni da cewa, Mista Thabane na yunkurin tserewa daga kasar zuwa Afrika ta Kudu inda ya ce zai nemi magani bisa dalilai na rashin koshin lafiya.

An dai soma ne da zargin Mae-saiah Thabane matar firaministan da kisan tsohuwar matarsa wato Lipolelo Thabane a shekara ta 2017 ta hanyar bindigewa, kwanaki biyu kafin a rantsar da shi a  mukamin Firaministan kasar.

Ya dai kasance Firaministan kasar na farko da ake zargi da hannu a laifin kisa, sai dai ya sanar da bukatar sauka daga karagar mulkin kasar a karshen watan Julin bana, bayan shan matsi daga jam'iyya mai mulkin kasar.