1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boris Johnson ya killace kanshi

November 16, 2020

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya killance kanshi a ranar Litinin bayan ya gana da wani dan majalisar dokoki Lee Anderson da ya kamu da cutar corona.

UK Boris Johnson
Hoto: David Cliff/NurPhoto/picture-alliance

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan Brexit inda Birtaniya ta ce tana kan bakarta tare da fatan cimma yarjejeniyar kasuwanci da kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin zaman kilace kai, Firaminista Johnson daga gidansa zai ci gaba da amfani da kafar sadarwa ta bidiyo wato Zoom da wasu kafofi yayin da ake gabar karshe ta tattaunawar Brexit a birnin Brussels.

In dai ba a manta ba a watan Afrilun da ya gabata ne dai Boris Johson ya shiga halin rai kwakwai mutu kwakwai sanadiyyar kamuwa da cutar corona.