1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Firaministan Burtaniya Sunak ya nemi a kwace kadarorin Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 25, 2024

Firaministan Ukraine Denys Shmygal ya bukaci kasashen na yamma da su yi amfani da kadarorin Rasha da kundisu ya kai Dala biliyan 300 don sake gida kasarsa

Hoto: Stefan Rousseau/AFP/Getty Images

Firaministan Burtaniya Rishi Sunak ya bukaci Kasashen Yamma da su yi ta maza don kwace kadarorin Rasha sannan kuma su agazawa Ukraine, da nufin girgiza shugaban Rasha Vladmir Putin.

Karin bayani:Rishi Sunak ya zama sabon firaministan Birtaniya

Jawabin na sa na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekaru biyu da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, yana mai jan hankalin kasashen G7 da su kwace kadarorin Rasha na kasashensu su sayar su aike wa Ukraine kudin, kamar yadda jaridar Sunday Times ta Burtaniya ta wallafa a Lahadin nan.

Karin bayani:Macron da Sunak za su yi aiki tare

Firaministan Ukraine Denys Shmygal ya bukaci kasashen na yamma da su yi amfani da kadarorin Rasha da kudinsu ya kai Dala biliyan 300 don sake gina kasarsa.