Firaministan Faransa ya yi watsi da soke wasu ranakun hutu
September 14, 2025
Talla
A wata hira da manema labarai firaministan ya ce akwai bukatar bijiro da wasu hanyoyin samar da kudaden shiga don farfado da komadar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.
Faransa dake zama kasa ta biyu mafi girma a tattalin arzikin yankin kasashe masu amfani da kudin Euro, yanzu ita ce kasa ta uku dake da dimbin bashi bayan kasashen Girka da Italiya.
Gibin kasafin kudin kasar na wannan shekarar ya kai kashi 5.8%, sama da kaso 3% na abin da kasashen EU suka amince.
A farkon makon nan ne majalisar dokokin Faransa ta kada kuri'ar yanke kauna ga Firaminista Francois Bayrou, watanni tara bayan ya dare kan madafun iko.
Karin Bayani:Faransa ta shiga wani wadi na tsaka mai wuya a siyasa