1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Coronavirus ta hana firamnistan Italiya zuwa Afirka

Suleiman Babayo USU
April 18, 2022

Firamnista Mario Draghi na kasar Italiya ya soke ziyara zuwa kasashen Afirka na Angola da Congo-Brazzaville sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

Italien Rom | Mario Draghi während Pressekonferenz
Hoto: Domenico Stinellis/AP/picture alliance

Firaminista Mario Draghi na kasar Italiya ya soke ziyarar aiki da aka tsara a kasashen Angola da Congo-Brazzaville, bayan gwaji ya nuna ya kamu da cutar coronavirus.

A wannan Litinin ofishin firamnistan ya bayyana haka, inda sanarwar ta ce  Draghi dan shekaru 74 da haihuwa ya nuna alamun kamuwa cutar ta coronavirus gabanin tafiya birnin Luanda na Angola ranar Laraba mai zuwa da kuma birnin Brazzavill na Congo ranar Alhamis, domin tattauna samun makamashin daga kasashen domin maye gurbin wanda kasar Rasha ke mayarwa.

Yanzu dai Luigi Di Maio ministan harkokin wajen kasar ta Italiya da ministan kula da muhalli Roberto Cingolani za su yi tafiyar a madadin firaministan.