1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan:Firaminista Shinzo Abe ya yi murabus

Abdullahi Tanko Bala
August 28, 2020

Firaministan Japan Shinzo Abe ya yi murabus daga mukaminsa saboda rashin lafiya bayan shafe tsawon shekaru yana fama da ciwon kumburin hanji

Japan Premirminister Shinzo Abe erklärt Rücktritt
Hoto: Reuters/F. Robichon

Firaministan na Japan Shinzo Abe ya sanar da cewa zai yi murabus saboda larurar rashin lafiya da yake fama da ita.

Yace yana fama da ciwon kumburin hanji kuma saboda kamarin ciwon ba zai iya samun sukunin gudanar da aikinsa na firaminista ba.

Yayin da aka dade ana rade radi game da rashin lafiyar musamman bayan da ya fita zuwa asibiti har sau biyu domin duba lafiyarsa kan ciwon da ba a baiyana ba, murabus din firaministan, ya zo da mamaki.

Abe yace zai cigaba da gudanar da aiki har zuwa lokacin da za a zabi sabon firaminista.