Fumio Kishida ya tsallake rijiya da baya
April 15, 2023![Japan | Zwischenfall beim Besuch von Fumio Kishida in Wakayama](https://static.dw.com/image/65331743_800.webp)
Talla
An jefi Firaministan Japan Fumio Kishida konson bam na hayaki yayin da yake dab da gabatar da jawabi a wajen wani taron yakin neman zabe a a garin Wakayama da ke gabashin Japan a wannan Asabar.
Firaministan dai bai sami rauni ba kuma 'yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi bayan aukuwar lamarin.
A watan Yulin bara ma haka aka harbi tsohon firaministan kasar Shinzo Abe inda ya sami mummunan rauni a lokacin da yake gabatar da jawabi a birnin Nara.