1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Firaministan ya aje aiki

Abdul-raheem Hassan
January 15, 2020

Murabus din Dmitry Medvedev na zuwa ne bayan kudurin Shugaba Vlamir Putin na yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul, domin tsawaita wa'adin mulkinshi.

Russland - Vladimir Putin und Dmitry Medvedev 2011
Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Firaminista Dmitry Medvedev da ya yi murabusHoto: Imago/ITAR-TASS

Firaministan Rasha da majalisar ministocinsa sun mika takardun ajiye aikinsu ga Shugaban kasar Vladmir Putin a wani mataki da suka kira na bai wa shugaban damar tabbatar da manufarsa na kwace karfin ikon majalisar dokoki da firaminista.

Tuni dai Shugaba Putin ya gabatar da sunan shugaban hukumar tattara harajin kasar Mikhail Mishustin mai shekaru 53, a matsayin sabon firaministan kasar. Masana na danganta matakin Shugaba Putin din a matsayin sharar fage na makomar siyasarsa, bayan ya kammala wa'adin mulki a 2024.