1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sudan: Firaminista Hamdok ya yi murabus

January 3, 2022

A cikin jawabin talabijin da ya yi wa 'yan kasar Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya ce yunkurinsa na dinke barakar da ke tsakanin 'yan siyasar kasar bai yi nasara ba.

Sudan Khartoum | Premierminister zurückgetreten | Abdalla Hamdok
Hoto: Mahmoud Hjaj/Anadolu Agency/picture alliance

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus daga mukaminsa a daidai lokacin da rikicin siyasa da zanga-zangar adawa da sojoji ke kara kamari a kasar. 

''A bisa wadannan hujjoji dana bayyana, na yanke shawarar yin murabus domin bai wa wani ko wata damar jagorantar kasar zuwa salon mulkin dimukuradiyya.'' inji Hamdok

Sai dai Hamdok ya yi gargadin cewa halin da kasar ke ciki abu ne mai matukar hatsari ga makomarta. Tun dai dawo da shi mukaminsa a watan Nuwamba da sojoji suka yi bayan juyin mulkin watan Oktobar 2021, Abdalla Hamdok bai bayyana sunayen ministoci ba, lamarin da ya jefa Sudan cikin rashin tabbas.