1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Italiya ta kaddamar da bikin taronta da shugabannin Afirka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 29, 2024

To sai dai shugaban kungiyar hadin kan Afirka Moussa Faki Mahamat, ya shaidawa taron cewa kamata ya yi a ce Italiya ta fara tuntubar Afirka tun kafin ta kai ga shirya taron, kuma lallai a cika duk alkawarin da aka dauka

Hoto: Remo Casilli/REUTERS

Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta kaddamar da bikin bude taron kasarta da shugabannin Afirka a wannan Litinin a birnin Rome fadar gwamnatin kasar, inda ta bayyana aniyarta ta bijiro da shirye-shiryen da za su bunkasa nahiyar Afirka, don dakile kwararar 'yan ci rani da kuma kyautata harkokin makamashi, da kuma yaukaka alaka tsakanin Turai da Afirka.

Karin bayani:Italiya ta shirya taron koli da shugabannin kasashen Afrika

To sai dai shugaban kungiyar hadin kan Afirka Moussa Faki Mahamat, ya shaidawa taron cewa kamata ya yi a ce Italiya ta fara tuntubar Afirka tun kafin ta kai ga tsara wannan shiri haka, kuma lallai akwai bukatar cika duk wani alkawari da ake dauka, ba wai fada a baki kadai ba tare da cikawa ba kamar yadda ake gani a wasu lokutan.

Karin bayani:Italiya ta samu firaminista mace ta farko

Shugabannin kasashen Afirka 24 ne dai suka halarci taron, da ke mayar da hankali kan batun tsaro da tattalin arziki da zai samar da aikin yi a Afirka, tare da kawo karshen kwararar 'yan ci rani masu tsallakawa zuwa Turai ta barauniyar hanya.