1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Ziyarar firaministoci daga Turai

Suleiman Babayo LMJ
March 16, 2022

Firaministocin kasashen Poland da Jamhuriyar Chek da kuma Sloveniya sun kai ziyara birnin Kyiv na Ukraine da yaki ya tarwatsa, inda suka gana da Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar ta Ukraine domin nuna goyon bayansu.

Ukraine Kyiv | Ziyarar shugabanni daga kasashen EU | Mateusz Morawiecki da Jaroslaw Kaczynski da Petr Fiala da kuma Janez Jansa
Shugaban Ukraine ya gana da firaministocin Poland da Solovaniya da Jamhuriyar ChekHoto: Ukrainian Presidential Press Office/AP/picture alliance

Firaministocin uku sun kai ziyarar a daidai lokacin da Rasha take zafafa hare-haren kan manyan biranen kasar ta Ukraine, yayin da kutsen da ta kaddamar ya shiga mako na uku. Firaministocin kasashen uku na gabashin Turai da ke zaman shugabannin na farko da suka kai ziyara tun bayan kaddamar da hare-haren na Rasha, sun kai wannan ziyarar duk da kararrawar gargadi da ake ji a birnin na Kyiv kan yiwuwar kai hare-hare. Shugaba Volodymyr Zelensky wanda ya tarbi bakin, ya yi godiya kan irin kwazon da suka nuna ganin irin yadda kutsen Rashan ya janyo jami'an diflomasiyya na wasu kasashe suka fice daga kasar: "Akwai jakadun kasashen ketere da dama da suka fice daga Ukraine, sakamakon irin girman kutsen da Rasha ta kaddamar a kan kasarmu. Wadannan mutane da muke girmamawa shugabanni na kasashe masu 'yanci na Turai, ba sa jin tsoron komai. Sun fi jin tsoron makomarmu."

Shugaba Volodymyr Zelensky na UkraineHoto: Pressebüro des ukrainischen Präsidenten/AP/dpa/picture alliance

A cewar Firaminista Mateusz Morawiecki na Poland, ya dace su yi duk abin da za su iya wajen kawo karshen yanayin da ake ciki a Ukraine din. Shi ma Firaminista Janez Jansa na Sloveniya ya jaddada dacewar duba bukatar Ukraine kan zama mamba a kungiyar Tarayyar Turai cikin gaggawa, abin da ake ganin zai zama sako kan kutsen na Rasha. Firaminista Petr Fiala na Jamhuriyar Chek ya ce suna sane da cewa 'yan Ukraine suna gwagwarmaya ba domin kansu kadai ba. Tuni firaministocin da suka kai wannan ziyara birnin na Kiev na kasar ta Ukraien suka koma gida, inda suka nuna fatan cewa ziyarar za ta kara azama kan samar da taimakon da Ukraine take bukata. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin fararen hula 700 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine, kuma akwai yiwuwar alkaluman za su haura haka. Kimanin mutane miliyan uku, sun tsere daga kasar zuwa gudun hijira a kasashen ketere.