Fitaccen mawaƙin Senegal ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugabancin ƙasa
January 3, 2012A ranar 26 ga watan Fabarairun ne aka shirya zaɓen shugaban ƙasa a Senegal. Kawo yanzu aƙalla 'yan takara sama da 15 ne suka bayyana sunayensu domin fuskantar shugaba mai ci yanzu wato Abdullahi Wade wanda zai yi takara a karo na ukku. Daga ciki har da fitaccen mawaƙin nan Yussuf N'dour wanda ya bayyana manufarsa ta tsayawa takara a wani taron manema labaran da ya kira a farkon watan nan a gidan telebijin na TFM mallakarsa. Youssou N'dour dai ya yi suna matuƙa gaya a duniya baki ɗaya gurin raira waƙoƙi, musamman a ƙasar ta Senegal, inda ya ce ya amsa kiraye-kirayen maza da mata, yara da manya 'yan ƙasar da ke buƙatar ya aza takararsa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, kamar yadda Atuman Dio magatakardan ƙungiyar ƙwadago a Senegal ke cewa.
"Abun murna ne, tun da mu ma'aikata ba za mu nunawa wani ma'aikaci ƙiyaya da adawa ba musamman mutumin da ke kawo tashi gudunmuwa a fannoni da dama irin na samar da ayyukan yi ga matasa, kada mu manta yana da kamfanoni da dama, kenan abu ne mai kyau hasali ma abu ne da ya kamata."
An dai jima ana rade-raɗin aza takarar mawaƙin har ma a ƙasahen waje inji Edward Ouedrago ɗan ƙasar Burkina Faso dake a cibiyar Gerdes.
"Youssou N'dour na Senegal, da ma akwai wasu alamomin da ke nuna hakan za ta faru, ka ga a daura da waƙoƙi, yana maida hankali ga samar da ayyukan yi ga matasa, kuma mutum ne da ke sauraren talakawa, ya kuma buɗa kamfanonin yaɗa labarai da dama, kai dai ni na goyi bayansa."
Yanzu haka dai ya rage ga 'yan ƙasar magoya bayansa da su nuna masa ƙauna a cikin akwatin zaɓe a ran 26 ga watan Fabarairu mai zuwa. Koda yake wasu na ƙorafin cewa baida ilimi mai zurfi. A lokacin da ya ke magana a taron manema labaran cewa ya yi.
"I gaskiya kuma haƙiƙa ban yi wani dogon karatu ba balantana a yi maganar ilimi mai zurfi a gurina. To amman ni a sanina matsayin shugaban ƙasa, ba wai digri ne ke ba da shi ba, a'a kuzari da manufa da kuma Allahn da ke buƙatar ka da shi, musamman a wannan lokaci na zaɓen demokraɗiyya."
To sai dai masu nazarin al'ammuran ƙasar na ganin cewar, shugaban ƙasa Abdullahi Wade ɗan shekaru 85 da haifuwa, wanda kuma Jam'iyarsa ta PDS ta tsayar a matakin ƙarshe na ɗan takara, kan iya lashe zaɓen ba tare da ya fuskanci wata mumunar turjiya ba daga rukunin 'yan adawar ƙasar da ke tafiya tamkar ɗiyan marina wato kowa da inda ya dosa. Yanzu haka sama da Jam'iyu 30 ne suka yi wani haɗin gwiwa ciki har da Jam'iyar Usman Tanor Dieng, da ta Mustafa Niasse, Idriss Seck da nufin ƙalubalantar shugaba Wade. To sai dai ya zuwa yau ba su tsayar da mutumin da zai tsaya a matsayin ɗan takaran adawa ɗaya tilo ba. Matakin da kuma kan iya rugujewa a cikin 'yan kwanakin nan ganin cewa kowane daga cikinsu ya ja daga yana mai cewar shine ya fi cancanta ya tsaya da yawun haɗin gwiwar.
Yanzu haka dai Youssou N'dour shine mutum na biyu a Afirka daga cikin waɗanda suka yi fice a dandalin wasanni da suka aza takarar a zaɓen shugaban ƙasa. Ko a shekara ta 2005 a ƙasar Laberiya fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan nan Georges Wiya ya aza takararsa ta neman kujerar shugaban ƙasa.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal