Barazanar fitar bayanai sirri ga Amurka
April 11, 2023Talla
Bayanan da aka kwarmata kuma wadanda jaridar kasar Amurka ta New York Time ta wallafa sun hada da cikakken bayani a kan matakin inda aka kwana a game da yakin Ukraine a farkon watan Maris na 2023, da kuma motsin sajojin Ukraine da ke fafatawa a fagen daga musamman a birnin Bakhmout wanda dakarun Rasha ke matsa lamba domin karbewa sai kuma bayanai a kan na'urorin kakkabo hare-haren ta sama da fadar Kiev ke tunkaho da su wajen kare kanta.
A cewar John Kirby mai magana da yawun shugaban Amurka, an sanar da Biden wannan halin da aka shiga wanda ya jefa fadar White House cikin tsananin damuwa domin kubucewar bayanai babbar barazana ce da ka iya yin tasiri kan harkokin tsaron cikin gida na Amurka.