Fito na fito da Soji da 'yan Boko Haram
January 2, 2013Mai magana da yawun runduran ta JTF Laftanar Kanar Sagir Musa ya ce mutanensu sun yi ba takashi da 'yan bindigar ne a jiya Talata inda su ka samu nasarar karbe makamai daga hannu wasu daga cikinsu sai dai yayin arangamar, kakakin na JTF ya ce soja guda ya rasa ransa.
Laftanan Kanar Sagir Musa ya ce arangamar da su ka yi da 'yan Boko Haram din ta samo asali ne bayan da 'yan kungiyar su ka tada bam a wani shingen biciken ababan hawa na JTF inda soji su ka maida wuta.
Kawo wannan lokacin 'yan kungiyar ta Boko Haram ba su ce komai ba game da artanbun da sojin su ka ce sun yi da mutanen na su a jiya.
Rikici tsakanin 'yan kungiyar da jami'an tsaro a tarayyar ta Najeriya dai ta yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama musamman ma dai a arewacin kasar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman