Fito-na-fito tsakanin 'yan sandan Girka
September 6, 2012A wannan alhamis ne wasu 'yan sandan ƙasar Girka da ke boren nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati suka kafa shinge a hedikwatar 'yan sandan kwantar da tarzoma na ƙasar, inda suka hana wasu motocin safa-safa da ke ɗauke da 'yan sandan kwantar da tarzomar ficewa daga farfajiyar hedikwatar domin zuwa babban filin da 'yan sandan da ke boren ke shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a ƙarshen mako.
Taƙaddama dai ta ɓarke a lokacin da wasu 'yan sandan kwantar da tarzomar suka yi ƙoƙarin fatattakar takwarorin aikin su, waɗanda galibin su ke sanye da kaki, kana suke ta furta kalaman yin Allah wadai da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati ɗauke da allunan da ke yiwa hukumomin tofin Allah tsine.
Ɗaya daga cikin jami'an 'yan sandan da ke boren ya ce ba za su taɓa kyale motocin Bus-Bus na 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa garin Thessaloniki ba, wanda zai karɓi baƙuncin kasuwar baje kolin da a lokacin ta ne kuma masu bore suka shirya gudanar da wata zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun da gwamnatin Girka ke aiwatarwa.
Kazalika in anjima kaɗan ne wasu 'yan sanda da jami'an kwana-kwana ma za su gudanar da wata zanga-zangar adawa da shirin tsuke bakin aljihun a tsakiyar Athens, babban birnin ƙasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas