Fiye da mutane 200 sun hallaka a Turkiya
May 14, 2014Talla
Masu aikin ceto na kokori zakulo daruruwan ma'aikata da suka makale, lamarin ya faru kusan da garin Soma na yammacin kasar ta Turkiya, kuma an yi imanin akwai ma'aikata kusan a cikin wajen hakar ma'adinan lokacin da aka samu fashewar.
Ma'aikatar kula da makamashi ta kasar ta ce, an fito da kimanin mutane 360 zuwa sanyin safiyar wannan Laraba. Mahukuntan kasar ta Turkiya sun cewa akwai yuwuwar matsalar lartarki ta haifar da fashewar da kuma tashin gobarar da aka samu.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman