Fiye da mutane 3000 suka rasu a tekun Meditareniya a shekara ta 2014
December 24, 2014Talla
Mahukuntan kasar Italiya sun bayyana samun mutane 1,026 a raye sannan guda biyar a mace a yayin wani sintirin aikin ceto da suka yi a tekun Meditareniya cikin sa'oi 24 da suka gabata.
A cewar mahukunta an shigar da gawar wani mai gudun hijirar zuwa jirgin Etna na sojan Italiya daga wani jirgin 'yan kasuwa, yayin da aka shigar da wasu matattun hudu a jirgin sintirin Orione na Cyprus.
Hukumar da ke lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a farkon wannan wata cewa kimanin masu neman tsallakawa Turai da ke ratsawa ta tekun na Meditareniya 3,419 sun halaka tun daga watan Janairu, abin da ya sanya wannan hanya ta zama mafi hadari wajen lakume rayukan mutanen.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo