Fiye da yara dari sun rasu a harin Taliban a Pakistan
December 16, 2014Bayan da wasu sojojin sakai na Kungiyar Taliban suka kai farmaki a wata makaranta da soja ke lura da harkokinta a ranar Talata a Pakistan, ya zuwa yanzu fiye da mutane 120 suka rasu , harin da ya zama cikin mafiya muni a kasar ta Pakistan.
Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun bayyana wannan hari da girgiza makarantar sojan da ke a arewa maso yammacin garin Peshawar, inda mayakan suka rika shiga aji zuwa aji suna ruwan harsashe ga daliban da basu ji ba basu gani ba.
Wani rashe na Kungiyar ta Taliban na Tehreek e- Taliban, sun bayyana daukar alhakin wannan hari da suka bayyana da cewa an tsara cewa maharan su sami daliban da suka dan tasa.
Firayim Minista Nawaz Sharif bayan Allah ya yi wadai da wannan hari ya bayyana shi da zama babban bala'i ga kasar kuma babbar asara ga kasar.
Tuni dai shugabannin kasashen duniya suka fara Allah wadai da wannan farmaki.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo