Flynn: Mahawara kan amsa laifin yin karya
December 2, 2017Talla
Mai shekaru 58 da haihuwa kuma janar na soja mai ritayan, ya kasance jami'in gwamnati mafi girman mukami, da ake zargi dangane yiwuwar hannun Rasha a zaben Amurkan na 2016.
Tsohon jami'in, ya bayar da bayanan karya ne ga hukumar binciken manyan laifukan Amurka ta FBI, a binciken da aka gudanar cikin watan Janairun wannan shekarar, dangane da tattaunawar da jakadan Rasha ya yi a karshen watan Disambar bara, mai alaka kai tsaye da zaben Amurkan.
Michael Flynn ya taka rawa lokacin yakin neman zaben shugaba Donald Trump, kuma fadar White House ta ce shi kadai ne wannan laifi ya shafa.