1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Francis Halzen ya lashe kyautar Nobel ta Physics

Binta Aliyu Zurmi
October 6, 2026

Masanin kimiyyar lissafi Francis Halzen ya lashe lambar yabo ta Nobel ta kimiyyar Physics, sakamakon bincikensa kan wasu sinadarai da ke taimaka wa masana wajen fahimtar sirrin sararin samaniya.

Schweden Stockholm 2026 | Bekanntgabe des Nobelpreises für Physik an Francis Halzen
Hoto: Christine Olsson/TT/picture alliance

Kwalejin Kimiyya ta Sweden ta ce binciken Halzen ya taimaka wajen gano neutrinos, wato kwayoyin zarra masu matukar kankanta masu karfin makamashi da ke fitowa daga sararin samaniya.

Halzen, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 82 da ke aiki a Jami'ar Wisconsin-Madison ta Amurka, ya ce bai yi tsammanin samun kyautar ba, yana mai yaba wa sauran masana da suka taimaka wajen gudanar da binciken.

Ayyukansa sun kuma taka muhimmiyar rawa wajen gina cibiyar binciken IceCube Neutrino Observatory da ke Antarctica, wadda ke amfani da na'urori da aka dasa cikin kankara.

Kyautar ta kunshi kronor miliyan 12 kudin kasar Sweden, kwatankwacin Euro miliyan daya.

Karin Bayani: Tarihin kyautar Nobel a takaice