Francois Bozize ya arce zuwa Kamaru
March 26, 2013Tun can da farko an riƙa baza labarin cewar tsohon shugaban ya arce zuwa Jamhuriyar Kwango tare da iyalensa, bayan da yan tawayen suka ƙwaci iko da birnin Bangui da kuma fadar shugaban ƙasar. To amma lokacin kaɗan sai aka samu labarin cewar gwamnatin Kamaru ta ba da sanarwar ta hayar kafofin yaɗa labarai cewar Francois Bozize yana a Yawunde.
Sanarwar da gwamnatin Kamaru ta bayyana a kan kafofin yaɗa labarai
Wata yar jaridar ta gidan talbijan da rediyio na ƙasar ta Kamaru wato CRTV ta bayyana sanarwar ta na mai cewar gwamnatin Kamaru ta na kira da a dawo da kwanciyar hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayan wani juyin mulkin da sojojin suka yi wanda ya kifar da gwamnatin Francois Bozize. A ƙarshe kuma ta ce sanarwa gwamnatin na cewar shugaban ya samu mafuka a Kamarun. Hukumomin na Kamaru sun samarwa da tsohon shugaban masabki a cikin wani babban Hotel ɗin da ke a birin Yawunde.
Wata motar soji ce ta ɗauki tsohon shugaban ƙasar Francois Bozize zuwa Hotel Hilton da ke a birnin Yawunde, Inda aka yi masa masabki. Kuma jama'a sun yi dandazo a bakin Hotel ɗin suna kallon yadda sojojin suka zagaye ginin na Hotel ɗin, kowane na furta albarkacin bakinsa. Cyprain Awudu Mbaya wani dan Majalisar Dokoki ne. Ya ce : '' Na yi ido huɗu da Bozize ya ce na ga lokacin da sojojin da ke tsaron shugaban ƙasa suka kawo wani mutumin a Hotel ɗin wanda muka gano cewar hamɓarraren shugaban Afirka ta ta Tsakiyar ne.''
Jama'ar ƙasar na bayyana fargaban su akan zuwan tsohon shugaban
Ƙasar ta Kamaru na raba iyaka mai girma da Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya, kuma daman kusan zaman doya da man ja ake yi tsakanin ƙasashen biyu, a farkon shekarar bana yan tawayen na ƙungiyar Seleka sun tsallaka suka shiga Kamarun inda suka kashe sojoji guda uku a garin Kenzu. Ɗan majalisar dokoki Cyprain Awudu ya ce suna da fargaba. Ya ce :'' Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakai masu tsauri domin kare iyokokin mu, ya ce wannan nauyi ne da ya rattaya akan wuya gwamnati.''
Wannan dai ba shi ba ne ,karo na farko da wani hamɓarraren shugaba na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da yake neman mafukar siyasa a Kamaru, tsohon shugaban ƙasar ma, da aka yi wa juyin mulki a shekarun baya wato Ange Felix Patase ,shi ma ya nemi mafuka a Kamaru a wani lokacin.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal