Ganawar Steinmeier da Sall a Dakar
February 21, 2022Talla
Shugaban kasar Jamus Frank Walter Steinmeier ya isa birnin Dakar na Senegal a wata ziyara aiki ta kwanaki uku da ya soma tun daga jiya Lahadi, a wannan Litinin aka shirya cewa shugaban zai gana da takwaransa na Senegal kana shugaban kungiyar tarayyar Afirka Macky Sall.
Daga cikin batutuwan da ake sa ran za su tattauna, har da na shirin samar da alluran riga-kafi na Covid 19 da Senegal za ta fara. Wannan ita ce ziyara ta biyu da wani shugaban kasar Jamus ya ke yi a kasar Senegal, Shugaba Steinmeir zai karkaré ziyarar tasa a ranar Laraba mai zuwa.