1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najejeriya: Fafutukar yaki da tsangomar Fulani

Uwais Abubakar Idris AH
April 1, 2021

A Najeriya wasu kungiyoyin kare hakkin jama’a da na Fulani, sun fara wani yunkuri neman kawo karshen matsalar tsangwama da nuna duk wani Bafulatani makiyayi a matsayin mai garkuwa da jama’a da satar shanu a kasar.

Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Kabilar Fulani makiyaya sun kasance a tsaka mai wuya a Najeriyar saboda wannan matsala ta garkuwa da jama’a domin fansa da ma kai hare-hare, inda ko dai bisa kuskure ko kuma da gangan don cimma wata manufa aka sanya su a gaba da tsangwama da nuna masu ‘yar yatsa a kan su ke aikata wannan laifi. Da zarar an buda baki maganar Fulani makiyaya ake yi da dangata su da wannan aika-aika duk cewa ta bayyana a fili cewa akwai wasu kabilu da ke aikata wannan. Sun dai kai ga bara a yunkuri na rarrabe aya da tsakuwa musamman a kan na baya-baya nan da ya faru a Jihar Benue. 

Fulanin sun dade suna fuskantar tsagoma a Najeriya
Wannan matsala ta nuna tsangwama da dora laifi na aikata miyagun laifuffuka a kan wata kabila a Najeriyar al’amari ne da aka dade ana fuskanta tun lokacin yakin basarar Najeriyar a shekarun 1962 da aka dorawa ‘yan kabilar Igbo ya zuwa lokacin da aka samu masu tada kayar baya a yankin Niger Delta, yanzu kuma ga Fulani makiyaya na faruwa.Ta kai ga hatta shanun da suka mallaka fulanin ba su tsira ba da wannan kyama da nuna tsangwama inda ake karkashe su da sanya masu guba a yanayi na tsanantar nuna kyama. Akwai dai dimbin kungiyoyin farar hula da suka shiga cikin wannan aiki a kokari na wayar da kan jama’a  hatsarin da ke tattare da nuna tsangwama da karan tsana ga Fulani. Gwamnatin Najeriyar dai ta bayyana cewa tana daukan matakai na kawar da nunawa wata kabila ko jinsi tsangwama a matsayin mai aikata laifi a kasar. 

Hoto: DW/K. Gänsler