1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fursunoni 57 sun mutu a Brazil

Abdul-raheem Hassan
July 30, 2019

Hukumomi sun tabbatar da asarar rayuka bayan barkewar yamutsi tsakanin bangarori biyu a gidan yarin da ke Altamira a arewacin kasar.

Brasilien Aufruhr in Gefängnisse
Hoto: Reuters/S. Pereira

Gidan talabijin na kasar Brazil ya nuna hotunan bidiyon tirnikewar hayaki daga gidan yarin, tare da fursunoni makale a saman rufin kwano. Hukumomi sun ce har yanzu ba a kammala tantance gawarwakin wadan da suka mutu ba, sakamakon tiririn wuta a yawancin dakunan.

Ma'aikatar kula da harkokin shari'a ta kasar ta ce mataki na gaba shi ne kawar da shugaban 'yan daban daga gidan yarin. Rikici a gidajen yari a Brazil ba sabon abu bane, inda fursunoni suka yi ta mutuwa a baya sakamakon tashe-tashen hankula da ake dangantawa da cunkoson jama'a.