1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fushin matasa na kara tsananta gabanin zabe a Tunisiya

September 24, 2024

A daidai lokacin da ake ci gaba da daukar matakan murkushe 'yan adawa a Tunisiya, matasa sun fara yin tururuwa a kan tituna. Ko zanga-zangar za ta iya kawo sauyi gabanin babban zabe na uku bayan juyin-juya halin 2011?

Matasa na yawan yin zanga-zanga a Tunisiya sakamakon waharlalun da suke fuskanta
Matasa na yawan yin zanga-zanga a Tunisiya sakamakon waharlalun da suke fuskantaHoto: Chedly Ben Ibrahim/NurPhoto/picture alliance

A yayin babban zaben kasar karo na biyu da aka gudanar a 2019 wanda kuma ya biyo bayan juyin-juya halin kasar na shekara ta 2011 da ya kifar da gwamnatin kama-karya ta marigayi Zine El Abidine Ben Ali, dan takarar indifenda da ya kasance farfesa wato Kais Saied ya lashe zaben da kaso 72 cikin 100. Ya dauki alkawarin magance cin-hanci da rashawa da kawo gyara a kasar, baya ga samar da kyakkyawar makoma ga matasa. Sai dai shekaru biyar bayan hawansa kan karagar mulki, har yanzu ba ta sauya zani ba, inda matasan da suka kasance mafiya rinjaye cikin wadanda suka zabe shi suka fara juya baya ga shugaban kasar mai shekaru 66 a duniya.

Karin bayani: Dimukuradiyya ko kama-karya a Tunusiya?

Shugaban Tunisiya Kais Saied ya dauko salon mulkin kama karyaHoto: Tunisian Presidency/APA Images/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Wael Faleh matashi, dan fafutuka daga wata kungiyar farar hula na da ra'ayin cewa: "Bayan shekaru biyar na mulkin Shugaba Kais Saied, yanayin rayuwar al'umma ya kara tabarbarewa, wannan babban abin takaici ne. Ban yi zabe a 2019 ba, na mika takardata ba tare da na zabi kowa ba. Al'umma ba sa samun aikin yi kuma ba su da 'yanci, babu abin da ya sauya, kawai suna yaudarar mutane ne."

Shekaru biyu bayan ya dare kan madafun iko, Shugaba Saied ya fara amfani da karfin ikonsa ba bisa ka'ida ba. Tun daga shekara ta 2021 kawo yanzu, ya tarwatsa al'amuran siyasa da dama na kasar baya ga daure 'yan jarida da lauyoyi da kuma 'yan adawa. Tunisiya na kan gaba cikin kasashen da suka kulla yarjejeniya da kasashen Turai, domin dakile kwararar bakin haure da 'yan ci-rani. Ko da Wassim Hammadi da ke zama mamba a jam'iyyar adawa ta PCD, sai da ya ce yanayin siyasar kasar ba wai kawai karfafa gwiwar yin hijira yake ba; har ma da hana mutane sha'awar shiga a dama da su a harkokin siyasa da ma shiga cikin al'umma saboda tsoro da fargaba.

Karin bayani: Zanga-zangar bakar fata a kasar Tunisiya

Bakin haure sun shiga cikin mawuyacin hali bayan da Tunisiya ta kulla yarjejeniya da EUHoto: Hasan Mrad/Zuma/picture alliance

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi tir da matakin murkushe 'yan adawar da yake yi, abin da ake kallon a matsayin wani mataki da yake dauka a kokarinsa na son yin tazarce. Romdhane Ben Amor da ke zama  Kakakin kungiyar kare hakkin dan Adam ta FTDES ya koka kan rashin 'yancin dimukuradiyya a Tunusiya, inda ya ce: "Babu wata niyya a siyasance domin gudanar da 'yantaccen zabe a karkashin tsarin dimukuradiyya. Kotu na yanke hukunci kan 'yan takara, abin da ke nuni da cewa shirye-shiryen zaben ka iya fuskantar barazana. Abu ne mai yiwuwa kotu ta soke duk wasu matakai da ke da alaka da shirye-shiryen zabe a kasar."

Karin bayani:Yarjejeniyar EU da Tunisiya kan 'yan gudun hijira

Cikin 'yan takara 17 da suka tsaya, 14 daga cikinsu ko dai an cire su daga jerin 'yan takarar ko kuma an daure su a gidan kaso. Koda yake a watan Agustan da ya gabata kotu ta mayar da 'yan takara uku daga cikinsu, Sai dai wata kotu a garin Jendouba da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar ta daure guda daga cikin wadanda a baya aka amince su yi takara Ayachi Zammel da ke zaman jagoran jam'iyyar adawa ta Azimoun tsawon watanni 20 a gidan kaso.