Fyade: Mata tsofaffi na rayuwa cikin fargaba a Kenya
July 18, 2017Mata tsofaffi 'yan sama da shekaru 60 da ke zaune a ungwannin marasa galihu sun dukufa wajen samun horo a fannin dubarun dambe domin kare kansu daga fyade daga wasu maza masu dauke da cutar AIDS ko SIDA a bisa wani canfi da ya taso tsakanin al'ummar kasar Kenya da ke cewa saduwa da mata masu yawan shekaru, na sa a samu waraka daga cutar ta SIDA da ma sauran wasu cututuka.Wannan ne ya sa wasu mata hudu dattijawa 'yan shekaru tsakanin 53 zuwa 65 mazauna ungwannin 'yan rabbana ka wadata mu na kewayen birnin Nairobi ke fita don samun horo a fannin damben zamani a wani fili na bakin garin birnin na Nairobi inda a kowane mako suke haduwa sau biyu suna koyon dubarun kare kai ta hanyar nakaltar fasahar dambe, ana iske wadannan tsaffin mata na bai wa hammata iska abin da kamar ban dariya sai dai su a wajensu ba batun wasa ba ne domin batu ne na kare kai kamar yadda Veronica 'yar shekaru 65 daya daga cikin matan ta tabbatar.
Wannan matsala ta yi wa matan masu yawan shekaru fyade ta samo asali ne daga wani canfi da ya yadu a tsakanin al'ummar kasar da ke cewa tarawa da tsohuwar mata na warkar da cututuka a cewar Leah Obanda wata 'yar fafutikar kare hakkin mata a kasar ta Kenya."Sun yi imanin cewa matar da ta shafe shekaru sama da 60 a duniya tamkar budurwa ce wacce ke ci gaba da rukon budurcinta domin ta jima ba ta sadu da namiji ba, kuma tarawa da ita na warkar da cutar Sida alhali ba gaskiya ba ne amma wannan hujja ce kawai suka fake da ita suna yi wa tsaffin mata fyade tare da kwace musu dukiyoyinsu. Kuma ga shi babu tsaro a ungwanin marasa galihun na bayan gari inda rayuwa ta kasance cike da hadari"
Yanzu haka dai tun bayan da ta soma koyan dabarun damben, Jane daya daga cikin wadannan mata ta ce ta yi nasarar korar wani daga cikin mazan da ya yi yinkurin yi mata fyaden a yayin da a nata bangare Veronika mai shekaru 65 ta ceto diyarta daga hannun wani namijin da shi ma ya yi yinkurin yi mata fyaden. Kuma wadannan nasarori biyu da suka samu ta iya kare kansu daga fyaden mazajen ta hanyar amfanin da karfin dantsensu ya kara ba su kwarin gwiwar ci gaba da horas da kansu kan dubarun damben musamman kasancewa nan da watanni biyu masu zuwa kasar Kenya ke shirya zaben 'yan majalisar dokoki wanda kuma ga ala'ada ake samun tashin hankali a lokacin ganin akasarin masu yi wa matan fyade na amfani da rudanin siyasa da ke faruwa a wannan lokaci domin kai wa dattijan matan harin da ma yi masu fyaden.