1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

G20: Scholz ya jaddada goyon baya ga Isra'ila da Ukraine

November 18, 2024

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada goyon baya ga Ukraine na kare kanta daga hare-haren Rasha tare kuma alwashin ci gaba da bada tallafin kudi wajen cimma wannan manufa.

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz Hoto: Ebrahim Noroozi/AP/picture alliance

Shugaba Scholz ya sanar da hakan ne a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai gabanin taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20.

Karin bayani: Zelensky na fatan kawo karshen yaki da Rasha a 2025 

Shugaban ya kuma kare matsayarsa na bai wa Isra'ila tallafin makamai da kuma goyon baya inda yace Isra'ila na da damar kare kanta daga duk wata barazana duk da cewa matakin na Jamus na shan suka daga kasashe da dama.

Karin bayani: Joe Biden ya yi kira ga Jamus da ta kara tallafa wa Ukraine

Shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva na son a tattauna batun yakin Ukraine a wajen taron na G20 duk da cewa bai aike da goron gayyata ga shugaban Volodymyr Zelensky na Ukraine ba, amma ya gayyaci Rasha inda Ministan Harkokin Waje Sergei Lavrov ke wakiltar kasar.