1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20: Za a kara wa manyan masu kudin duniya haraji

July 27, 2024

Shugabar asusun IMF mai bayar da lamuni a duniya Kristalina Georgieva ta yi maraba da yunkurin kara wa masu kudi harajin, tana mai cewa matakin ya zo a lokacin da ya dace.

Hoto: India's Press Information Bureau/via REUTERS

Ministocin kudi na kasashen G20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya sun amince su kara wa manyan masu kudi a kasashensu haraji. Wannan ita ce babbar matsayar da suka cimma a yayin taronsu na kwanaki biyu a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

Sanarwar da kasashen suka fitar ta ce rashin daidaito tsakanin talakawa da masu kudi na kawo matsala ga tattalin arziki tare da kara jefa wani rukuni na mutane cikin fatara.

Shugaban Brazil  Luiz Inacio Lula da Silva shi ne kan gaba wajen bai wa kasashen na G20 shawarar kara wa masu dukiyar harajin. Shugaban na bukatar a kara musu kaso 2 cikin 100 na harajin da suke biya, wanda hakan ke nuna manyan attajiran duniya 3000 da ke zaune a kasashen G20 za su biya dala biliyan 250 sabanin dala biliyan 200 da suke biya a duk shekara.