G5 Sahel ta yi tir da sanya mata harin kunar bakin wake
December 9, 2016Mata wakilai daga kasashe biyar na yankin sahel da suka hada da Chadi da Moritaniya da Mali da Burkina Faso da kuma Niger mai masauki a karkashin kungiyar G5 Sahel sun yi nazarin matsalolin tsaro da suka addabi yankin da kuma hanyoyin da za a bi domin kawo karshen matsalar.
Musamman kungiyar ta nuna matukar damuwa kan yadda kungiyar Boko Haram ke amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake da lalata musu rayuwa
Madam Habibu Hasiya Issa, jami'a a hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya ONU ta yi tsokaci kan yadda irin wadannan kungiyoyin ta’adda ke sace yara 'yan mata kanana suna yi musu fyade da kuma sanya su harin kunar bakin wake inda suke salwantar da rayuwarsu da ta sauran jama'a.
A nata bangaren wakiliyar kasar Chadi, Madam Appoli Motalbai babbar sakatariya a ofishin ministan matan kasar, ta ce akwai babban kalubale a gaban al’umma, inda ta bukaci kowa ya bada gundunmawarsa wajen inganta tarbiyyar yara domin ganin basu shiga cikin kungiyoyin bata gari ba.
Ita ma da take tsokaci Dr Joustie Koulidiatie, wakiliya daga Burkina Faso ta baiyana damuwa yadda ta ce ake mayar da mata saniyar ware a al’amuran raya kasa, tana mai cewa mata su ne ginshikin al’umma a saboda haka akwai bukatar damawa da su a dukkan al’amura na ci gaban kasa.