1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu ci gaba kan cinikayya a taron G7

Ramatu Garba Baba
June 9, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke halartar taron koli na kasashen duniya masu karfin tattalin arziki na G7, ta ce sun kama hanyar cimma matsaya a zaman taron da suka yi kan cinikayya a kasar Kanada.

G7 Gipfel in Charlevoix Kanada
Hoto: twitter.com/RegSprecher

Merkel a zantawa da manema labarai, ta ce sun amince da su bayar da goyon baya ga sharudda da aka shimfida kan dokokin kasuwancin duniya. Taron kolin ya gudana ne a daidai lokacin da a ke ci gaba da takkadama a kan shinge da karin harajin da Amirka ta dora kan karafa da goran ruwa da kawayen cinikin kasar da suka hada da wasu kasashen Turai da Kanada da kuma Mexico.

Shugaban na Amirka Donald Trump, ya katse zamansa a wurin taron, inda ya zarce zuwa kasar Singapore don zaman tattauna da shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un kan makamin nukiliya,za a yi ganawa mai dimbin tarihi ne a ranar 12 ga watannan na Yuni, Trump ya musanta rahotannin cewa, taron na kungiyar G7 ya kasance mai tattare da takaddama.