1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine: G7 ta yi fatali da bukatar Rasha

March 28, 2022

Ministocin Faransa da Jamus da Italiya da Amirka da Birtaniya da Kanada na kallon bukatar hakan da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi a matsayin  saba wa yarjejeniyar sayar da makamashi da ke a tsakaninsu.

Belgien | G7-Gipfel im NATO Hauptquatier in Brüssel
Hoto: Sean Kilpatrick/The Canadian Press/AP/picture alliance

Gaggan kasashe masu karfin tattalin arzikin nan guda bakwai na G7 sun yi watsi da bukatar Rasha ta daga yanzu su rika sayen makamashin iskar gas da takardar kudin Rasha ta ''ruble''. Ministan kula da makamashi na Jamus  Robert Habeck ne ya shaida wa 'yan jarida haka a wannan Litinin.

Masana tattalin arziki sun ce dabara ce da Shugaba Putin ke da ita a yunkurinsa na ganin ya tayar da komadar darajar takardar kudin Rasha ta ''ruble'' wace ta fadi tun bayan mamayar da ya yi wa kasar Ukraine. 

Kasar Rasha ce dai ke zama babbar mai samar da makamashin iskar gas ga galibin manyan kasashen duniya masu arziki na G7, inda suke amfani da gas din wurin dumama dakuna a lokacin hunturu da kuma samar wa da kansu lantarki.