1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sake fasalta harajin duniya daga G7

Abdoulaye Mamane Amadou
June 4, 2021

Ministocin kudi na kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki G7 sun soma wani taron kolinsu a karon farko a zahiri tun bayan bullar annobar corona da zimmar sake fasalta haraji.

England London | G7 Treffen der Finanzmininster(inn)en
Hoto: Stefan Rousseau/AP/picture alliance

Taron birnin Landan zai tattauna ne kan batun sake fasalta harajin duniya, tare da duba yiwuwar cimma matsaya kan kudaden harajin da kamfanoni musamman ma da ke amfani da fasahohin zamani ke bayyanawa, inda ministan kudin Birtaniya Rishi Sunak, ya ce yana da kyau a yi wa batun kallo da idon basira yana cewa "Ina da yakinin cewa wannan taro zai kasance mana wata dama ta tinkarar muhimman kalubalai a cikin gagawa da ke addabar tattalin arzikin duniya." Ko baya ga batun harajin duniya taron zai kuma duba batun raba daidai na allurar rigakafi a kasashen duniya, kana kuma taron dai na a matsayin wani na share fage ne kan wani taron kolin kasashen da za su gabatar a ranar 11 ga wannan watan wanda ake hasashen shugaban Amirka Joe Biden zai halarta.