1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

G7 za ta sasanta rikicin yankin Gabas ta Tsakiya

Binta Aliyu Zurmi
October 2, 2024

Kungiyar kasashen mafiya karfin arziki a duniya G7 ta sha alwashin aikin kafada da kafada da bangarorin da ke gaba da juna a yankin gabas ta Tsakiya domin dakile rikicin yankin da ya rincabe.

Deutschland Münster | Flaggen G7
Hoto: Wolfgang Rattay/AFP/Getty Images

Kungiyar ta G7 ta ce maslaha ta hanyar diplomasiyya abu ne mai yiwuwa a wannan rikicin.

Firaministan Italiya Giorgia Meloni wace kasarta ke shugabantar kungiya a wannan shekarar, ta tattauna da takwarorionta ta wayar tarho biyo bayan harba rokoki da Iran ta yi a Isra'ila.

A wata sanarwar da ofishin Firaminsta Meloni ya fitar, an ruwaito tana cewar rikicin ba zai amfani kowa ba don haka akwai bukatar su mayar da wukaken su kube domin samun zaman lafiya.

Da kakausar murya mahukuntan na Italiya gami da takwarorinsu na Jamus da Faransa da Birtaniya da Amirka suka yi tir da harin na Iran a Isra'ila.

G7 ta duba yiwuwar sake laftawa Iran takunkumi biyo bayan wannan harin, sai dai a nashi bangaren Shugaba Biden ya ce baya goyon bayan kai hari a tsahar makamashin nukiliyar Iran.