1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabatad da funafunan bidiyo ga matasan Kenya.

YAHAYA AHMEDNovember 22, 2006

A kwanakin bayan ne dai aka kammala wani taron ƙasa da ƙasa a birnin Rom na ƙasar Italiya, don tattauna irin rawan da kafofin sadarwa ke takawa, a ayyukan raya ƙasashe masu tasowa. A cikin muhimman jigogin da taron ya yi nazari a kansu, har da yadda za a sanya jama’a, su da kansu, su ba da labaran da suka shafi halin rayuwarsu na yau da kullum, da irin gwagwarmayar da suke yi, ba tare da wani daga waje, ya zo ya rubuta maƙala ko sharhi a kansu ba. Ta hakan ne dai aka ƙiƙiro wani shiri na ɗaukan funafunan bidiyo, waɗanda yaran da ke zaman kashe wando na birnin Nairobin ƙasar Kenya suka ɗauka da kansu, don bayyana yadda suke rayuwa a kan titunan birnin.

A unguwannin talakawa da marasa galihu na birnin Nairobin ne aka zaɓi yara matasa, maza da mata, waɗanda suka ɗau funanfunan unguwarsu da kuma matsugunansu don bayyana yadda su da kansu ke ganin halin rayuwarsu da kuma na mazuna yankunan. Elisabeth, na ɗaya daga cikin matasan da ake kira “yaran titi“ a birnin, waɗanda funanfunasu ya sami lambar yabo. A cikin nata fim ɗin, ta ba da tarihin kakarta mace ne, mai shekaru 105 da haihuwa, wadda har ila yau take nan da ranta a ƙauyen Kiabu, kusa da birnin na Nairobi. Elisabeth ta ce tun tana ƙarama ne ta baro ƙauyensu, ta zo birnin, ba ta da kowa, sai sauran yara irinta a kan titi. Sabili da haka, ko makaranta ma ba ta zuwa. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

„Saboda ni mace ce, ina da matsala da dama da na yi ta fama da su. Da farko dai, akwai haɗarin yin ciki, ba kamar yara maza da su ma ke zaune a kan titin ba. Bugu da ƙari kuma, zan iya kamuwa da cutar AIDS. Ba ni da wata sana’a. Amma yanzu da aka koya mini yadda zan iya ɗaukar funafunai da na’urar bidiyo, ina matuƙar farin ciki ƙwarai. Ga shi dai mun ɗau funafunai da dama.“

Wata ƙungiyar sa kai, mai suna African Medical and Research Foundation, ko kuma AMREF a taƙaice, wadda aka kafa tun 1957 a birnin na Nairobi, ita ce ta ɗau nauyin gabatad da wannan shirin, don bai wa yaran titunan wata dama ta koyar sana’a, wadda za ta ba su damar iya kula da kansu, su fice daga wannan ƙangin zaman banza na kashe wando, wanda a ƙarshe shi ne ke sanya su shiga cikin wani mugun hali na shan ƙwayoyi da karuwanci, har ma da aikata laifuffuka daban-daban kamar sace-sace da fashi da makamai da dai sauransu.

Wani yaro, Henry, mai shekaru 16 da haihuwa, wanda shi ma ya ci moriyar wannan shirin ya bayyana gamsuwarsa ne da cewa:-

„Tun shekaru 7 ne na ke rayuwa a kan titi, amma babu abin da nake yi takamaimai. Saboda a kan titin, babu abin da mutum ke tabukawa, sai shan taba da ƙwayoyi iri-iri, haka kawai, wato ana zaman kashe wando. A cikin wannan halin dai nake, har lokacin da jami’an wannan ƙungiyar, kamarsu John Muirurui, suka zo mana suka gayyace mu zuwa yin wasan ƙwallon ƙafa. Mun gamsu ƙwarai, kuma abin ya ba mu sha’awa. Daga bisani ne kuma suka gayyace mu zuwa cin abinci a wani ƙaramin otel. Ai ran nan na ji daɗi sosai, saboda ban taɓa zaton cewa, ni ma wata rana zan iya cin abinci a nan ba. Kafin wannan lokacin dai, a bola nake samo abin da zan saka a ciki.“

Ƙungiyar dai a hankali ne ta yi ta shawo kan yaran titi kamarsu Henry, don su sake halin rayuwa, a kuma ba su damar zamowa mutane na gari, waɗanda su ma za su iya ba da gudummowa ga aikin gina ƙasa. Da farko dai, bayan ba su abinci, ƙungiyar na kuma ba su sabbin tufafi ne, kafin a fara koya musu yadda ake amfani da na’urorin ɗaukar funafunan bidiyon. Idan sun naƙalci duk yadda na’urar take da kuma irin dabarun da za a iya yi da ita, sai su fara ɗaukan funanfunai kan tarihin rayuuwarsu kawo wannan lokacin. A cikin ƙwazo da azamar da suke nunawa, waɗannan yaran na titi na iya wallafa funafunai kan halin rayuwarsu na yau da kullum, waɗanda kafofin sadaswa kamarsu talabijin ba sa iya yin irinsu. A lal misali akwai wani fim da ke bayyana yadda yara ke ta gwagwarmaya da yin doguwar tafiya a ƙasa, don neman abinci ko aikin ci rani, saboda ba su da kuɗin biyan motocin hawa ko babura don su kai su inda suke niyyar zuwa. Wani fim ɗin kuma, ya dubi irin mawuyacin halin da mata ke aiki ne a cikinsu a ƙauyuka da kuma babban birnin.

Ƙungiyar ta AMREF dai ta ce ta gamsu ƙwarai da irin sakamakon da take samu na cim ma nasarar shawo kan yaran titunan su sake halin rayuwarsu, har ma su fice daga kan titin gaba ɗaya. Duk waɗanda suka sami damar wallafa funafunai kan halin rayuwarsu, sun kuma yi tunani mai zurfi a kan yanayin da suka sami kansu a ciki, abin da ya buɗe musu wata ƙofar basira ta gano ko kuma samo hanyoyi daban-daban na canza da kuma inganta halin rayuwarsu. Ta hakan ne dai yara da yawa, kamar Elizabeth, suka sake shawara, suka koma ga iyalansu da kuma makaranta. Elisabeth dai ta ce sha’awar ababan duniya da iyayenta ba sa iya samar mata ne dalilin da ya sanya ta ƙaurace wa gida a ƙauyensu zuwa birnin Nairobi:-

„Abin da ya sanya ni ƙaurace wa gida, daga iyayena, shi ne ina ganin ababa da yawa da nake so, amma ba sa iya saye mini su. Sabili da haka ne, na yanke wa kaina shawarar zuwa birni. Amma a nan, sai a kan titi kawai nake rayuwa. Tunani dai a wannan lokacin shi ne, ba su damu da ni ba, saboda ba sa taimakona. Ni ma a nawa ɓangaren, sai na daina nuna musu biyayya. Sai aka shiga cikin wani halli na tsamari, inda sukan yi mini duka. Amma yanzu na gane cewa, ba laifinsu ba ne da ba sa iya sayo mini duk abin da nake bukata. Na kuma gane cewa, ba ni kaɗai ba ce ’yarsu. Muna da yawa, yaran da suka haifa. Yanzu dai ina farin ciki ƙwarai da ƙungiyar AMREF ta sake kawo ni gida ta haɗa ni da iyayena. Tun da farko dai kungiyar ta yi ta taimakonmu. Ta bam u abinci, da tufafi, da kayaan wasa. Daga bisani kuma ta nuna mana yin amfani da na’urorin bidiyo. Yanzu ina da abin da zan duƙufa a kai. Ba ni da lokacin yin wata rigima kuma da iyayena.“

Kamar dai Elisabeth, akwai yara da yawa da suka nuna gamsuwarsu da aikin wannan ƙungiyar da kuma yadda ta taimaka musu inganta halin rayuwarsu. Niko, wani matashi ne mai shekaru 17 da haihuwa. Shi ma na cikin yaran da ƙungiyar ANREF ɗin ta ceto daga kan titunan birnin Nairobi. Shhi ma ya wallafa fim ɗin bidiyo ne kan mahaifiyarsa, wadda ƙungiyar ta sake haɗa su. Shi ma ya bayyana cewa:-

„Rayuwarmu dai yana fara ne da mahaifiya, kamar yadda na bayyanar a fim ɗin. Saboda a ko yaushe, ita ce ke gefen mutum idan yana da matsala, ko a gefen hagunsa ko na damarsa. Ni dai burina ne, ta hanyar wannan fim ɗin, in ƙarfafa wa duk masu ƙauracewa daga gida gwiwa, na su koma gun iyalansu. Rigingimu ba su da wata fa’ida. Ina shawartarsu su guje shi, su duƙufa wajen inganta halin rayuwarsu.“

Yanzu dai Niko da Elizabeth da Henry, suna da kyakyawar makoma, wadda babu shakka ta fi na halin da suke ciki a da, yayin da suke kan titi. Suna kuma cikin waɗanda aka zaɓa su gabatad da funafunansu a taron ƙasa da ƙasa da aka gudanar a birnin Rom, kan muhimmancin kafofin sadaswa, wajen tafiyad da ayyukan raya ƙasashe masu tasowa. Su dai waɗannan matasan, da can baya kaɗan, suna tafiyad da halin rayuwarsu ne a kann titi, da shan ƙwayoyi, da neman abinci daga bola. Amma ga shi yanzu sun sami damar bayyana tarihinsu ta hanyar funafunan da suka wallafa da kansu, ga taron ƙasa da ƙasa. Bugu da ƙari kuma, a karo na farko sun sami damar fita daga yanayin da suka saba da shi, sun ga wata duniya daban a birnin Rom. Taron da ababan da suka gani a babban birnin na ƙasar Italiya dai, sun ba su sha’awa, inji Henry, wanda ya ce yana son ya koyi aikin ɗan jarida nan gaba. Amma ya yi nadamar cewa, ba a gayyato yara dama irinsu daga ƙasashe masu tasowa zuwa taron ba. Duk da hakan dai, saƙonsa ga sauran yara matasa na ƙasashe masu tasowa a duniya baki ɗaya, waɗanda har ila yau, ke cikin irin halin da su suka sami kansu kansu a ciki a da, shi ne:-

„Ga mu dai nan a taron ƙasa da ƙasa, amma ba mu ga yara matasa irinmu ba. Sabili da haka, muna son mu faɗa musu cewa, muna wakilcinsu a nan, su duka. Muna fatan cewa, su ma za su sami sauyi a halin rayuwarsu, dukkansu, ba na ƙasashhen Afirka kawai ba, na duk ƙasashe masu tasowa, ko’ina kuma suke a duniya.“