An nada firaministan rikon kwarya a Gabon
September 7, 2023Talla
Raymond Ndong Sima mai shekaru 68 ya taba rike mukamin firaminista a karkashin mulkin Bongo daga shekarar 2012 zuwa 2014
Daga baya ya zama mai kakkausar adawa da Bongo ya kuma yi takara da shi a zabbukan 2016 da 2023.
Sai dai bai tabuka abin a zo a gani ba a zaben baya bayan nan wanda sakamakon sa mai cike da rudani ya bai wa Bongo nasara wadda a karshe ta janyo juyin mulkin soji a kasar.
A waje guda wani mai shiga tsakani na kungiyar raya cigaban kasashen gabashin Afirka ya sanar da cewa gwamnatin mulkin sojin ta ce a shirye ta ke ta tsara jadawalin mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.