1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabon: Brice Oligui Nguema ya sha rantsuwar kama aiki

May 3, 2025

Shugaban Gabon Brice Oligui Nguema ya sha rantsuwar kama aiki, bayan kawo karshen mulki iyalan gidan Bongo da suka shafe shekaru 55 a kan madafun ikon kasar.

Shugaban kasar Gabon Brice Oligui Nguema
Shugaban kasar Gabon Brice Oligui NguemaHoto: Ken Ishii/AP/picture alliance

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Brice Oligui Nguema wanda yalashe zabe da kashi 95 cikin 100 na kuri'un da aka kada a watan Afrilun 2025, ya karbi madafun iko ne na tsawon shekaru bakwai, bayan majalisar mulkin sojin kasar na tsawon watanni 19 bayan ya kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo a shekarar 2023.

Karin bayani: Sojan da ya yi juyin mulki ya lashe zaben Gabon

A kalla shugabannin kasashe 16 suka halarci bakin rantsar da shi, yayin da dubban magoya bayansa suka yi ta bukukuwan murna  sanye da riguna dauke da hotonsa a filin wasa na babban birnin kasar. Gabanin Gabon ta koma kan cikakken kudin tsarin mulki, sai ta shirya zaben 'yan majalisar dokoki, wanda ake sa rai ya gudana kafin karshen bazara.

Shugaba Oligui Nguema mai shekaru 50 dai a yanzu na da jan aiki a gabansa, inda zai fuskanci kalubale na lalacewar ababen more rayuwa da talauci da kuma bashi da ya yi wa kasar mai arzikin mai katutu.