Gabon: Doka ta karfafa ikon shugaban kasa
January 11, 2018Majalisar dokokin kasar Gabon ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya tanadi kara karfin ikon shugaban kasa. Sabon kundin tsarin mulkin da ke zama na bakwai tun bayan kawo karshen tsarin mulkin jami'iyya daya tilo a kasar a shekara ta 1991 ya kunshi sauye-sauye a fannin tsarin zaben da na shugabanci inda ya tanadi gudanar da zagaye biyu a zaben shugaban kasa.
Sabon kundin tsarin mulkin ya kuma tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa zuwa shekaru bakwai , tare kuma da cire matakin da ke kayyade adadin wa'adin mulkin shugaban kasa da tsohon kundin tsarin mulkin ya kunsa.
Kazalika a karkashin sabon kundin tsarin mulkin, daga yanzu shugaban kasa kadai ne ke da wuka da nama wajen tsara manufofin siyasar kasar sabanin tsohon kundin tsarin mulkin kasar inda shugaban kasa ke tarayya da gwamnatinsa a cikin wannan hurumi. A nan gaba ne kotun tsarin mulkin kasar za ta yi nazarin sabon kundin tsarin mulkin da bayyana matsayinta a kansa.