Shekaru 55 na shugabancin gado a Gabon
July 9, 2023Mai shekaru 64 a duniya Shugaba Ali Bongo Ondimba ya bayyana hakan ne, a wani jawabi da ya yi ga dandazon magoya bayansa da aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook. A shekara ta 2009 ne dai, Bongo ya karbi shugabancin Gabon a hannun babansa Omar Bongo Ondimba da ya kwashe shekaru 41 a kan karagar mulki. Hakan dai na nuni da cewa, iyalan na Bongo sun kwashe shekaru 55 kawo yanzu suna mulki a Gabon. Koda yake da kyar Shugaba Ali Bongo ya sha a zaben 2016, inda ya dara abokin hamayyarsa Jean Ping da ya bukaci a sake zaben da kuri'u dubu biyar da 500 kacal. Sai dai duk da yadda jam'iyyun adawa ke ganin iyalan Bongo sun mayar da mulkin Gabon gadon gidansu, sun gaza fitar da mutum guda da zai iya fafatawa da Ali Bongo ya wakilce su a zaben da ke tafe. A yanzu haka dai, akwai 'yan adawa 15 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar shugabancin kasar.