1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Ali Bongo ya tsige mataimakinsa

Gazali Abdou Tasawa
May 22, 2019

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo, ya sauke mataimakinsa Pierre Claver Maganga Moussavou da kuma ministan muhalli da kare itatuwan kurmi na kasar Guy Mertrand Mapangou daga kan mukaminsu. 

Gabuns Präsident Ali Bongo
Hoto: Reuters/T. Negeri

Fadar shugaban kasar ta Gabon ta sanar da daukar wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya Talata. Sai dai ya zuwa yanzu a hakumance fadar ba ta bayyana wasu dalillan Shugaba Ali Bongo na daukar wannan mataki ba. 

Amma dai matakin tsige mataimakin shugaban kasar  na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar da dama ke ta sa kira ga shugaban kasa na ya sauke mataimakin nasa da ministan muhalli da kula da itatuwan kurmin na kasar wadanda ake zargi da hannu a wata badakalar fataucin itatuwa masu daraja wadanda dokar kasar ta haramta kisansu.